Wednesday 8 March 2017

Sanusi Lamido Sanusi: Ba zan taba tunanin barin sarauta na saboda ofishin gwamnati- Sarkin Kano

Ku dena haihuwan ʼƴaʼƴa kamar kayyayaki

Gwamnan ya bada wannan sanarwar a 9 Maris, 2017, a taro tare da waƙilan united nations a daƙin taron sa.

Gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno ya bayyana cewa, ayyukan Boko Haram a jihar Borno,  ta haifa marãyu sama da 52.301 haɗe da 52.911.

Gwamnan ya bada wannan sanarwar a 9 Maris, 2017, a taro tare da waƙilan united nations a daƙin taron sa.

Shettima ya ƙara cewa yan ta'addar sun hallaka ajin karatu sama da 3,335, Ginin birni 665, gidaje 956,456, gidan wutan lantarki guda 201, da Asibitoci.

Gwamna Shettima ya bayana cewa,shugabanci da jagoranci mai kyau,hallitar sabon aiki, ilimi tare da Noma za su iya canza hallakar da ƴan ta’addar suka kawo.

Jakada Mathew Rycroft shine ya jagoranci tawagar mutane 14 da suka yi wa gwamnan ziyara.

Gwamnan, ya ba da alamar cewa , gwamnatin sa ya hau sabuwar tsare tsare wanda zai taimaka wa mutane, da kuma rage girman matsalar talauci, ya ce babu abin da ya shafi boko haram da musulunci.



Related Posts

Sanusi Lamido Sanusi: Ba zan taba tunanin barin sarauta na saboda ofishin gwamnati- Sarkin Kano
4/ 5
Oleh

Subscribe via email

Like the post above? Please subscribe to the latest posts directly via email.