– Tsohon Ministan shiri na kasa, kuma tsohon shugaban hukumar PPPRA ya sayi gidan Naira Miliyan 836.8 a Panama
– Bayanai akan Gbadomosi sun fito ne daga takardun Panama
Jaridar Premium Times ce ta gano kudaden da tsohon Minista, Gbadomosi ya boye a kasar Panama. Jaridar ta samu taimako ne daga Kamfanin shari’a na Mossack Fonseca, wadda ta toni asirin masu hali wadanda suke boye kudaden su a Panama domin kin biyan haraji a kasahen su.
KU KARANTA: Sojoji sun ga abun mamaki a sansanin yan Boko Haram
A cewar bayanai da aka samu, Ministan ya sayi gidan ne a 2008 a lokacin ya yake shugabantar PPPRA, ya sayi gidan akan Dala Miliyan 2.6, inda aka sanya sunan Ciclones Corporation a matsayin masu gidan.
Rahotannin sun bayyana cewa Gbadamosi ya aiki wani yaron shi a cikin jirgi inda yaje ya duba gidan.
Gida na farko yana da fadin 537,33 square meters, a hawa na 35 da 36, darajar shi takai N436,800,000. Gidan na 2 yana nan a Ocean park Tower yana da girman 479,88 square meters. Darajar shi takai Naira Miliyan 400.
A unguwar da Ministan ya sayi gidan, tana daya daga cikin unguwanni mafi kyau, tsada, da kuma tsaro a kasar ta Panama. Akwai filayen kwallo, da sauran ab ubuwan more rayuwa. Masu gidaje a wurin ana basu damar kin biyan haraji har na tsawon shekaru 20 kafin su fara.
A wani labarin kuma, hukumar EFCC ta bayyana cewa ta gano sama da Dala Biliyan 12.9 waddanda aka sace a karkashin mulkin Jonathan. Hukumar ta bayyana cewa tana cigaba da kokarin kwato kudaden inda ta amshe wasu gwalagwale daga hannun tsohuwar Minsitar Mai, Diezani Alison Madukwe, da sauran wasu tsofaffin jami’an gwamnatin data shude.
Hukumar kuma ta wanke Mai shari’a Danladi Umar na kotun CCT daga zargin da ake yi mashi na rashawa.
The post Tsohon Minista Najerioya ya sayi gida mai tsada a Panama appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.