– Hukumar NSCDC ta jihar Bayelsa ta bayyana cewa ta lalata wasu haramtattun matatun Mai
– Desmond Agu, Kwamandan NSCDC na jihar Bayelsa ya bayyana haka
– Ya bayyana cewa zasu kara himma wajen lalata hramtattun matatun na Man
Jami’an NSCDC
Sama da haramtattun matatun Mai 400 hukumar NSCDC ta jihar Bayelsa ta wargaza daga watan Junairu zuwa na Maris na wannan Shekarar.
Wannan na zuwa a cigaba da fusknatar wahalar Mai da akeyi a Tarayyar Najeriya.
Desmond Agu ya bayyana cewa sun wargaza haramtattun matatun Man lokaci lokaci domin hana su cigaba da aikin da suke yi.
Yace “Muna nan a koyaushe domin kare muhimman abubuwa na Mai. Wannan runduna a shirye take da ta hukunta masu haramtacciyar sana’ar mai da sana’ar su.
Agu ya bayana cewa sun tsananta bincike ne a bakin iyakar gabar ruwan Najeriya inda ska kama wani shugaban tsagerun Nija Delta da kuma yaran shi.
Inda yake magantawa akan bututun mai na AGIP wanda yake a karamar hukumar Kudancin Ijaw, ya bayyana cewa sun kama wasu masu laifi inda suka hannata su zuwa wajen yan sanda domin abun ya wuce hurumin su.
Idan za’a iya tunawa, a kwanakin baya, wasu mutane 3 sun rasa rayukan su bayan da wani bututun Mai ya fashe inda ya kone su a Olugboboro dake karamar hukumar kudancin Ijaw. Zauren matasan Ijaw sun nemi gwamnatin Tarayya data halarta kananan matatun mai da al’ummar yankin ke kafawa.
A wani labarin kuma, rundunar sojin Najeriya take tankar yaki a wata karamar hukuma dake a cikin Jihar Rivers. Wannan yazo ne bayan da wasu matsafa sukayi kokarin amshe karamar hukumar bayan sun kashe wani soja a jihar Bayelsa.
Hukumar soji ta sha alwashin hukunta dukkanin masu tada zanne tsaye ko kuma kokarin haddasa rigima a yankin na Nija Delta.
The post Hukumar NSCDC ta wargaza haramtattun matatun Mai appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
from Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM http://ift.tt/20sNG9p
via IFTTT
