Sunday, 10 April 2016

APC ta jihar Kwara: Masu tugumar saraki baza suyi nasara ba

– APC ta jihar Kwara ta bayyana cewa masu tugumar Saraki baza suyi nasara ba

– Jam’iyyar ta bayana cewa suna neman suna ne kawai

– Ta zarge su da neman bata ma Saraki suna

Clifford Ordia, senator representing Edo Central has disclosed that Senate President Bukola Saraki has the support of PDP senators but should he be convicted by the CCT, the PDP would produce his successor.

Shugaban majalisar Dattawa Saraki

Jam’iyyar APC ta jihar Kwara ta bayyana cewa masu so suga an kulle shugaban makjalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki baza suyi nasara ba.

Jami’i mai hudda da jama’a na jam’iyyar  APC ta jihar Kwara, Alhaji Sulayman Buhari ne ya bayyana haka inda ya bayyana cewa masu tugumar tashi suna yin haka ne kawai domin su samu suna. Jaridar Leadership ta ruwaito labarin.

Buhari yace ” Bisa la’akari da yadda aka fara shari’ar, kai kace suna da wani abu wanda zasu iya kama Bukola Saraki da shi. Amma awanni 48 bayan fara shari’ar ya nuna cewa basu da wani abu akan shugaban majalisar Dattawan. Idan ma sunyi haka ne domin su bata sunan Bukola Saraki, toh baza su cinma nasara ba domin suma basu da kimar da za’a kalle su.

A cewar jam’iyyar APc ta jihar, bayan da suka gano cewa basu da wani abu wanda zasu iya kama Saraki dashi, kawai sai suka maida abun wasa.

Jam’iyyar ta bayyana Saraki a matsayin gwarzan namiji wanda bai karaya ba duk da cewa ana so a kawo shi kasa.

Saraki yana fuskantar tuguma ne daga hukumar CCB a kotun CCT akan rashin bayyana kaddarorin shi a lokacin da yake gwamnan Jihar.

Haka Zalika hukumar EFCC ta bayyana cewa tun saukar Saraki gwamnan Kwara, har yanzu yana karbar kudaden albashin wata-wata daga gwamnatin Jihar.

A wani labarin kuma, takardun Panama sun nuna cewa shugaban majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki nada kudade makudai aje a kasar ta Panama. Manyan mutane daga kasashe daban daban na duniya na boye kudade a kasar ta Panama domin guje ma biyan haraji. Bayan fitar wannan rahoto ne wasu mutane suka fara zanga-zanga a kasar Iceland wanda ya sanya Firayim Ministan Kasar yayi murabus bayan da takardun suka tona mashi asiri.

The post APC ta jihar Kwara: Masu tugumar saraki baza suyi nasara ba appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.



from Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM http://ift.tt/1oOcvie
via IFTTT

Related Posts

APC ta jihar Kwara: Masu tugumar saraki baza suyi nasara ba
4/ 5
Oleh

Subscribe via email

Like the post above? Please subscribe to the latest posts directly via email.