Saturday, 30 April 2016

Ku karanta abinda shugaban hukumar yan sanda ce game da yan bunburutun

– Shugaban hukumar yan sanda a kasar Najeriya mai suna Sifeto Janar Solomon Arase yace wanda za’a hana aikin bunburutun

– Wani dan jarida mai suna Ibrahim Ma’azu Mada Bakenawa ya rahoto wanda dokar hana bunburutun ta fara aiki a jihar Zamfara

Wani labari take fitowa ta bayyana wanda, ana ci gaba da karfafa dokar hana bunburutu da babban sifeton yan sandan Najeriya Solomon Arase ya yi, ta fara aiki gadan- gadan a jihar Zamfara.

KU KARANTA KUMA:

Yau dai teburan yan bunburutun sun zama tabkar kufai kowa ya kama kansa.  A garin Gusau, wani babban birnin jihar ta Zamfara, ya zama babu ko da mutum daya da ya nuna kangare wa dokar. Haka abun ya ke a sauran kananan hukumoni goma sha hudu da ke fadin jihar.

bunburutu

Yan bunburutu

Jama’a dai da dama na bayyana kalamai mababbanta, inda wasu ke bayyana goyon bayansu, wasu kuma na sukar matakin.

Alhasan Yusuf Argungu yace wanda, mataki ne mai kyau Allah yasa mafi zama alkhairi a kasa.wato abinda ke faruwa ,sunakara sa mai yayi tsada,da algus yajan sayarwa jama,a.sa manja da kananzur da jawa.kana gidan mai a zubamusu kai a haka. Allah ya kyauta.

Nasir Yar Aduwa yace wanda, duk wata doka da za,asa akan talaka take karewa mai neman na abinci ga kuma matsi na halin rayuwa,dan Allah matasa kukara yadda ayi amfani daku wajen bangan siyasa.

Umar Abubakar Umar yace wanda, irin cigaban kenan irin chanjin kenan amma a kullum Nigeria mukan kama abunda baida amfani a garemu shine muke bashi muhimmanci ga abunda zai amfane mu sai mukiyale shi.

The post Ku karanta abinda shugaban hukumar yan sanda ce game da yan bunburutun appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.



Related Posts

Ku karanta abinda shugaban hukumar yan sanda ce game da yan bunburutun
4/ 5
Oleh

Subscribe via email

Like the post above? Please subscribe to the latest posts directly via email.