Saturday 30 April 2016

Abun mamaki: Ga wani Coci da canza zuwa Makarantar Islamiyya a Afirika ta Kudu (hoto)

Jaridar Rariya ta rahoto wanda, nan ba da dadewa ba za a sauya cocin nan mai dadadden tarihi na Dutch Reformed da ke Langlaagte a Johannesburg babbar birnin kasar Afrika ta Kudu, zuwa makarantar Islamiyya.

Rabaran Hennie van Rooyen ya shaida wa manema labarai cewa an saida cocin ga wasu Musulmai ne saboda kula da cocin na matukar cin kudade masu yawa.

makarantar islamiyya

Wani Coci da ta canza zuwa Masallaci

Ya ce kodayake ba haka aka so ba amma kuma ba su da halin kashe makudan kudade don ci gaba da kula ginin cocin.
Kuma baya ga haka, Rabaran din ya ce yankin da cocin ya ke duk kabilar Indiya ta mamaye wurin.

KU KARANTA KUMA:

Shi kuwa Bishop Ryan Sooknunan wanda a can baya ya kan yi hayar majami’ar domin gudanar da wasu harkokinsa na ibada, ya zargi Rabaran Hennie van Rooyen da cocin Dutch Reformed da saba wa yarjejeniyar da ke tsakaninsu sakamakon sayar da cocin da suka yi. Don haka ne ya sha alwashin daukar matakin shari’a da kuma shirya zanga-zanga don nuna adawa saida cocin da aka yi.

Sai dai a nan cikin harabar majami’ar akwai kabarin shugaban cocin na farko da na matarsa wadanda Rabaran Rooyen ya ce yana daga cikin yarjejeniyar da aka cimma a lokacin sayar da majami’ar cewa ba za a kawar da gurbin kaburburan ba ta yadda ga dukkan mai bu}atar ziyara ya na da damar ya shiga.

Bayanan wani ]an mujami’ar sun nuna cewa dukkan masu halartar cocin su watse face ‘yan kalilan da suka yi saura.

The post Abun mamaki: Ga wani Coci da canza zuwa Makarantar Islamiyya a Afirika ta Kudu (hoto) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.



Related Posts

Abun mamaki: Ga wani Coci da canza zuwa Makarantar Islamiyya a Afirika ta Kudu (hoto)
4/ 5
Oleh

Subscribe via email

Like the post above? Please subscribe to the latest posts directly via email.